Obama ya dawo da kotun soji a Guantanamo

Fursunoni a sansanin Guantanamo Bay Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Fursunoni a sansanin Guantanamo Bay

Shugaba Obama na Amurka ya amince a ci gaba da gurfanar da mutanen da ke tsare a sansanin Guantanamo a gaban kotun soji.

Manyan jami'an gwamnatin Obama sun ce ba su janye aniyyarsu ta rufe sansanin ba, to amma wannan mataki alama ce da ke nuna cewa za a jima ba a kai ga cimma hakan ba.

A watan Janairun 2009 ne dai, a mako na farko na shigarsa fadar gwamnatin Amurka ta White House, Shugaba Obama ya dakatar da kotunan na soji, ya kuma yi alkawarin rufe sansanin na Guantanamo, yana mai cewa za a yiwa wadanda ake zargi da kasancewa 'yan kungiyar Al-Qa'ida shari'a a kotunan farar-hula.

Sai dai zazzafar adawar da wannan manufa ta Obama ta fuskanta ta tilasta shi sake shawara, bayan Majalisar Dokokin kasar ta kada kuri'ar haramta kai wadanda ke tsare a sansanin cikin kasar ta Amurka.

'Yan jam'iyyar Republican dai sun sa kafar-wando guda da shirin yiwa tsararrun shari'a a kotunan fararen hula ne bisa dalilai na tsaro, yayinda wadansu 'yan jam'iyyar Democrat masu matsakaicin ra'ayi suka ji nauyin goya baya ga gwamnatin saboda suna gudun yin hannun-riga da ra'ayin akasarin jama'ar kasar.

Yayin da yake fuskantar zabe badi, shi ma dai shugaban na Amurka ya fahimci cewa inda baki ya karkata nan yawu ya ke zuba.

Shirin yin shari'a ga tsararrun a kotunan farar-hula ya fuskanci tsananin adawa ne daga masu tunanin cewa yin hakan na da hadari saboda kotunan ka iya wanke wadanda ake tuhuma daga duk wani laifi, sannan kuma cin fuska ne a baiwa wadanda ake tuhumar hakkoki irin na Amurkawa.

A halin yanzu dai akwai fursunoni dari da saba'in da biyu a sansanin na Guantanamo.