Jam'iyyun Najeriya sun kulla yarjejeniya

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar da wani taro tare da shugabannin jamiyyun siyasar kasar, inda ta gabatar da dokoki da tsare tsaren da jamiyyun za su yi aiki da su a zaben watan Afrilu, domin su sa hannu.

Manufar wannan kundi dai shi ne, samun tabbaci daga wurin jamiyyun siyasar, cewa ba za su yi wani wani abu da zai yi zagon kasa ga zabenda za a gudanar ba.

Sai dai wasu daga cikin jamiyyun siyasar ba su sanya hannu a kan kundin ba.

Taron dai ya fara ne cikin tsanaki har zuwa lokacinda aka fara kiran jam'iyyu su sanya hannu kan kundin.

Wasu jam'iyyun sun nuna cewa, babu wata dama da aka ba su don su gabatar da korafinsu game da kundin wanda suka ce tun a zabukan da suka gabata suke sanya hannu kan irin wannan kundi amma babu abinda ya sauya.

Daga nan ne shugaban jamiyyar NDP Chukwumerije ya fice daga dakin taron kuma ya yi jawabi ga manema labarai cikin fushi.

Ya ce; "Mu muka san irin abubuwan dake faruwa a jihohi, wasu daga cikin kwamishinonin hukumar INEC a jihohi, wasu jami'an hukumar sun nuna matsayarsu, kai shugaban hukumar zabe ba ka sani ba, kana zaune kana karbar rahotanni, rahotanninda ba su da sahihanci." In ji Chukwumerije

Da yake maida martani, Farfesa Jega ya ce an tado da wasu batutuwa wadanda wasu daga cikinsu gaskiya ne;

"Amma ina son nemi alfarma daga wurinku, kada mu hargitsa wannan lamari. Mun zo nan ne don batun sanya hannu kan kundin tsare-tsare da dokokin zabe, amma zan yi amfani da wannan dama na saurari dukkanin korafe-korafenda aka gabatar." In ji Jega.

"To saidai kada mu hargitsa lamarin, idan mun gama abinda ya kawo mu, sai mu saurari sauran batutuwan."

Kusan dukkanin jamiyyun Najeriya sun sanya hannu kan wannan kundin, in banda jamiyyar ARP.

Ita ma jamiyyar PDP mai mulkin kasar ba ta sa hannu kan wannan kundi ba, domin kuwa a lokacinda aka kira wakilinta wato Kawu Baraje, ba ya nan.