Yau take ranar mata ta duniya

Ana gudanar da bukukuwan cika shekara dari da zagayowar ranar mata a duk fadin duniya.

An fara bikin wannan ranar ne domin yin hamdala da irin ci gaban da mata suka samu, akan bambance-bambancen da aka rika nuna masu a wancan lokaci. Daruruwan mata Palasdinawa sun yi maci a Gaza inda suka yi kiran samun hadin kan Palasdinawa tare da kawo karshen rabuwar kan da aka samu tsakanin magoya bayan bangarorin siyasarsu biyu, wato Fatah da Hamas.

Yanzu haka mata a kasashe da dama sun ce suna da ikon fadin albarkacin baki a cikin harkokin kasashensu.

Daga cikin irin wadannan kasashe har da kasar Ghana inda mace ce ke shugabar majalisar dokokin kasar.

Haka kuma mace ce ke rikon mukamin Babbar Mai Shari'a a Kotun Kolin kasar .

Sai dai duk da irin wannan ci gaba Hajia Aisha Muhtari shugabar wata kungiya mai zaman kanta, wato Voice Network da ke fafutakar kare hakkin mata, ta ce a akwai sauran aiki a gaba saboda har yanzu mata na fuskantar sauran bambance bambance da kuma cin ma zarafi.

A jamhuriyar Nijar a tubarrakin wannan rana mata a birnin Maradi sun gudanar da jerin gwano har zuwa fadar gwamnatin jahar, inda suka mika takardar kukansu ga Sakataren gwamnatin wanda ya karbe su.

Cikin matsalolin da mata suka fi kuka da su a jahar ta Maradi har da ta rashin karatun 'ya'ya mata.