Yunkurin karshe na warware matsalar Ivory Coast

Wata wutar da aka cinna a Ivory Coast
Image caption Wata wutar da aka cinna a Ivory Coast

Yayin da yanayin tsaro ke kara tabarbarewa a Ivory Coast, kungiyar Tarayyar Afirka na yunkuri na karshe don gano bakin zaren warware rikicin siyasar kasar ta hanyar diflomasiyya.

Tashe-tashen hankula dai sai yaduwa suke yi a fadin babban birnin kasar, Abidjan, inda gungun matasa—wasunsu fuskokinsu a rufe, wasu kuma dauke da adduna—suka shata iyakoki a daukacin unguwannin birnin.

A yanzu haka dai wani hoton bidiyo da aka dauka da wayar salula ya bayyana a birnin, wanda ke nuna wadansu mutane biyu farar hula wadanda aka cinnawa wuta suna shure-shuren mutuwa.

Dubban iyalai kuma sun nemi sa'a ga zakara da nufin tsira da rayukansu, yayin da wadansu ke dogayen layuka a kofar bankunan da ba kowa a cikinsu da fatan samun albashinsu.

Mutumin da duniya ta ce shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar bara ya bar kasar ta Ivory Coast don halartar wata tattaunawa a hedkwatar Tarayyar Afirka da ke Habasha.

Sai dai abokin hamayyar Alassane Ouattara, wato Laurent Gbagbo, ba zai halarci tattaunawar ba.

Mutane kalilan ne dai a kasar ke sa ran za a iya warware wannan badakala ta hanyar diflomasiyya.

Kuma ko da yake aljihun Mista Gbagbo ya fara bushewa, babu alamun za a cimma maslaha cikin ruwan sanyi nan kusa.