An azabtar da ma'aikatan BBC a Libya

Feras Killani Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Daya daga cikin ma'aikatan BBC da aka kama, Feras Killani

An kama wadansu 'yan jarida masu aiki da Sashen Larabci na gidan talabijin na BBC su uku, aka kuma lakada musu duka a Libya yayin da suke dauko rahoto a kan rikicin kasar.

Ranar Litinin ne dai aka kama mutanen sannan aka rika yawo da su a barikokin soji da dama, inda aka rufe fuskokinsu aka sanya musu ankwa, aka kuma yi barazanar harbe su.

Kamar sauran takwarorinsu dai, tawagar 'yan jaridar sun yi yunkuri ne na kaucewa ka’idojin da gwamnati ta gitta su shiga garin Zawiyya, wanda a farkon wannan makon nan ya kasance a karkashin ikon 'yan tawaye amma daga bisani dakarun Kanar Gaddafi suka kai masa hari.

Bayan an tsare su a wani wurin bincike na sojoji na wani lokaci dai aka debe mutanen uku zuwa wani barikin soja da ke Tripoli, inda aka rufe fuskokin nasu, aka sanya musu ankwa, sannan aka ba su kashi.

Mai aikawa da rahotanni Feras Killani ya fi shan wahala saboda irin labaran da ya ke bayarwa na rikicin na kasar Libya.

Bayan an sake su, mutanen uku sun bayyana cewa sun zaci za a kashe su.

Sun kuma ce an jera su ana kwatanta bindige su har sau biyu, inda harsashi ya wuce ta kusa da kan daya daga cikinsu.

Sai dai ko da yake daya daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar ta Libya ya nemi gafara dangane da yadda sojoji suka tozarta mutanen, tuni 'yan jaridar uku suka fice daga kasar.

Karin bayani