Jiragen yakin kasar Faransa sun soma harbi a Libya

Birnin Benghazin kasar Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jiragen yakin kasar Faransa sun soma aikin kare fararen hula tun bayan da majalisar dinkin duniya ta zartar da kuduri akan kasar

Wani jirgin saman yaki na kasar Faransa ya kai hari a kan wata motar sojin Libya, a karo na farko na yunkurin da kasashen duniya suka shiga yi don aiwatar da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na kare fararen hula a kasar ta Libya.

Shugabankasar Faransa Nicolas Sarkozy yace jiragen kasarsa sun soma shawagi a sararin samaniyar Libya, domin kare fararen hula daga duk wani hari da za'a iya kai musu.

Ana kuma tsammanin ganin wasu jiragen yakin daga wasu kasashen duniya

Shugabankasar Faransan Nicolas Sarkozy yace aikin kasar Faransa ne ta taimaki al'ummar larabawa wadanda suke neman hakkokinsu.