Kotun Duniya ta ba da sammacin 'yan Kenya

Luis Moreno-Ocampo Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Babban mai shigar da kara Luis Moreno-Ocampo

Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya ta bayar da sammacin gurfanar da wadansu mutane shida wadanda ake zargin suna da hannu a tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shugaban kasar Kenya a shekarar 2008.

Mutanen sun hada da wadansu ministocin gwamnatin kasar su biyu wadanda aka dakatar daga aiki, da kuma tsohon shugaban ’yansandan kasar.

Kotun ta umurce su da su bayyana a gabanta a birinin Hague ranar bakwai ga watan Afrilu mai zuwa.

Babban mai shigar da kara na kotun, Louis Moreno Ocampo, ya ce ana zargin mutanen da aikata kisa, da korar mutane daga kasar, da kuma azabtar da mutane.

Mutane fiye da dubu daya ne dai suka rasa rayukansu yayin da sama da dubu dari uku suka rasa matsugunansu sakamakon tarzomar da ta barke bayan zaben shugaban kasa a Kenya.