Tukwicin kamo shugaban 'yan adawar Libya

Mustafa Abdel-Jalil Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Majalisar Kasa ta 'yan adawa, Abdel-Jalil

Yayin da kasashen duniya ke duba yadda za su bullowa rikice-rikicen da ake fama da su a Libya, gidan talabijin na gwamnatin kasar ya bayyyana cewa an tanadi tukwici ga duk wanda ya taimaka aka kama shugaban Majalisar Rikon Kasa wadda 'yan adawa suka kafa a Benghazi.

Gidan talabijin din ya bayyana cewa Ofishin Bincike a kan Manyan Laifuffuka na kasar zai bayar da dinar dubu dari biyar na kudin kasar, kwatankwacin dalar Amurka dubu dari hudu, ga duk wanda ya kama Mustafa Abdel-Jalil, wanda gidan talabijin din ya ce “dan leken asiri ne”.

Wanda ya bayar da bayanan da suka taimaka aka kama shi kuma, a cewar gidan talabijin din, za a ba shi tukwicin dala dubu dari da sittin.

Shi dai Mustafa Abdel-Jalil minista ne a gwamnatin kasar ta Libya kafin ya sauya sheka ya koma bangaren 'yan tawayen.

Shi ne shugaban majalisar rikon kwaryar da 'yan tawayen suka kafa a Benghazi da nufin samar da gwamnatin rikon kwarya wadda za ta jagorance su a siyansance.

Kafa majalisar a watan da ya gabata dai ya biyo bayan tattaunawa ne tsakanin jagorori masu adawa da gwamnatin Kanar Gaddafi.