Likitoci sun soma yajin aiki a Nijar

Kungiyar likitoci ta Niger, SYMPHAMED, ta shiga sabon yajin aiki na kwanaki 10 daga yau din nan, domin ci gaba da matsa wa gwamnati lamba na ta biya mata wasu bukatu.

Bukatun sun hada, samar da kayan aiki da magunguna a cikin asibitoci, da daukar sababbin kwararrun likitoci aiki domin cike gurbin da ke akwai, da kuma karin albashi.

A jiya likitocin sun yi wata ganawa da shugaban kasar Janar Salou Djibou, sai dai ba su cimmawa wani abu ba.

A karshen makon da ya gabata ne likitocin na Nijar suka kammala wani yajin aiki na kwanaki 7, a kan wadannan bukatun.