Shugaba Goodluck ya kai karar jam'iyyar CPC

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption CPC ta musanta hannu

An ba da rahoton wasu matasa a garin Gombe sun jejjefi tawagar yakin neman zabe ta shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, yayin da ya kai ziyara a can.

Haka kuma matasan sun yi kone-kone a kan tituna.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya zargi magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar CPC, Janar Muhammadu Buhari, da laifin lalata masa ofishinsa da ke jahar Gombe.

Shugaba Jonathann ya ce ya kai karar Janar Buhari da magoya bayan nasa a jahar ga hukumar zabe domin ta dauki matakin ladabtarwa a kansu.

Babban Sakataren kasa na jam'iyyar CPC, Alhaji Buba Galadima, ya din ta musanta zargin.

Jam'iyyar PDP ta jihar ta ki maida martani, ta ce al'amari ne gwamnati ba na jam'iyya ba.

Sai dai jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar ya ce su a saninsu babu wani abin da ya sami ofishin na jam'iyyar PDP