Kalubalen kasashen Afrika kan Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto afp getty
Image caption Magoya bayan Ouatara na zanga-zanga

Wasu shugabannin Afirka, a karkashin inuwar Tarayyar Afirka, suna yin taro a birnin Addis Ababa na Ethiopia, domin duba hanyoyin warware rikicin siyasar Cote d'Ivoire.

Masu lura da lamurra na ganin cewa, akwai rarrabuwar kawuna a tsakankanin shugabannin Afirkar, kan yadda za a tinkari matsalar.

Yayin da wasu ke kiraye-kirayen a kawo cikakken goyon baya ga Alassane Ouattara - wanda kasashen duniya suka ce shi ne halataccen shugaban Cote d'Ivoire - wasu kuwa suna da ra'ayin a kafa gwamnatin hadin gwiwa ne, tsakaninsa da shugaba Laurent Gbagbo.

Majalisar dinkin duniya wadda ita ce ta sa idanu akan zaben da aka yi a kasar a watan Nuwambar bara ta bayyana cewa Shugaban kasar Laurent Gbagbo, ba shi ne ya yi nasara ba, Alassane Outtara ne.

Gbagbo ya ki sauka

Sai dai kuma shi Mr Gbagbon ya ki sauka daga mulki.

Ya kuma ki amincewa da barin kasar, ko kuma kan cewa dakarunsa sun murkushe masu zanga-zangar adawa, ta hanyar amfani da bindigogi akan mutanen da basa dauke da makami.

Shugaban ya kuma haddasa kiyayya mai karfi a kudancin kasar, inda mutanen kudanci ke kyamar wadanda ke arewa dake zaune a can da kuma miliyoyin bakin dake zaune a can, inda suke muzguna musu tare da tayar musu da hankali.

Suma 'yan adawa sun mayar da martani ta hanyar shirya kansu, wanda ya sanya a halin yanzu ake ganin akwai matukar hadari kan cewa wani sabon yakin ka iya barkewa a tsakaninsu wanda kuma zai iya janyo makwabtan kasashe ciki.

Diplomasiyya

Wannan kuma na nuni da cewa karshen diplomasiyyar ka iya kasancewa mafarin rikici.

Shugabannin nahiyar Afirkan dake taro a birnin Addis Ababa na da zabi.

Zasu iya baiwa shugaban da aka zaba, wanda kuma ba shi ne a bisa mulki ba wato Alassane Outara goyon baya.

Amma kuma ba zasu taba gujewa yakin da ka iya biyo baya ba.

Ko kuma zasu iya zabar bin hanyar diplomasiyya ta hanyar kira domin aiwatar da gwamnatin hadin kan kasa.

Sai dai wannan ma ba lallai bane ya iya kawar da banbance-banbancen da ke tsakani, sannan kuma zai kasance wani cikas ga kasashen nahiyar Afirkan dake marawa tafarkin demokradiyya baya.

Akwai yiwuwar tabbas sai abubuwa sun rinchabe kafin su dawo su gyaru a kasar ta Ivory Coast.