Ana fargabar shiga yakin basasa a Libya

Rikicin Libya na kara muni Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Red Cross ta ce ana yakin basasa a Libya.

Kungiyar bayar da agaji ta duniya ta Red Cross ta ce Libya ta afka cikin yakin basasa.

Kungiyar ta yi gargadin cewar fararen hula na dandana kudarsu a tashin hankalin, kuma ba ta samun damar kai wa yankunan da fadan ya fi kamari.

Shugaban kungiyar ta Red Cross, Jakob Kellenberger, ya bayyana cewar abu ne da ba za a amince da shi ba cewar har yanzu an katse galibin kasar Libya daga samun taimakon jin kai, kwanaki 24 bayan fara rikicin.

Dakarun Kanar Gaddafi dai na ci gaba da kai hari a yankunan da ke hannun 'yan tawayen, suna yin ruwan bama bamai, a kusa da garin Ras Lanuf.