Faransa ta amince da 'yan tawayen Libya

Faransa ta amince da 'yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Faransa ce kasa ta farko da ta dauki irin wannan mataki

Kasar Faransa ta amince da gwamnatin da 'yan tawayen kasar Libya suka kafa, a matsayin halartacciyar gwamnatin Libya.

Ofishin shugaba Nicolas Sarkozy ne ya bada sanarwar, kwana guda bayan da 'yan Majalisar Tarayyar Turai suka nemi Tarayyar da ta amince da gwamnatin 'yan tawayen.

Babbar jami'ar hulda da kasashen waje ta Tarayyar Turai Baroness Ashton, ta ce babu wanda ya umarce ta da ta dauki irin wannan matakin.

Wani jami'in kungiyar National Libyan Council, wacce ta kafa gwamnatin 'yan tawayen, na fadi-tashin neman goyon bayan kasashen Tarayyar Turai.

Jami'an diflomasiyyar Tarayyar Turai sun shaida wa BBC cewa: "Muna bukatar sanin ko su wanene, kuma ko suna wakiltar 'yan tawayen kasar ta Libya.

Suka kara da cewa yana da mahimmanci ayi aiki tare da kungiyar Kasashen Larabawa.

Karin bayani