Nijar: Bayan juyin mulkin Fabrerun 2010

Nijer Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomin sojin kasar sun yi alkawarin maida ta kan tafarkin dmokuradiya

Abubuwa masu mahimmanci da suka faru a Nijar tun bayan juyin mulkin watan Fabrerun 2010, a daidai lokacin da ake shirin zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. 18 Fabreru 2010: Wani juyin mulki da sojoji suka yi ya hambarar da shugaba Tandja - Wannan ya kawo karshen rikicin da batun tazarcen shugaban ya haifar. 23 Fabreru 2010: Aka bayyana Manjo Salou Djibo a matsayin shugaban Majalisar mulkin sojin kasar.

1 Maris 2010: Aka kafa gwamnatin rikon kwarya ciki harda biyar daga cikin jami'an sojin da suka jagoranci juyin mulki.

31 Oktoba 2010: Aka kada kuri'a kan sabon kundin tsarin mulki da nufin maida kasar kan tafarkin dimokuradiyya. 25 Nuwamba 2010: Gwamnatin soji ta amince da kundin tsarin mulkin da jama'a suka amince da shi a kuri'ar rabagardamar da aka kada. 7 Janairu 2011: Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Al-Qaeda ne suka kama wasu Faransa wa biyu a Yamai, sannan suka kashe su a lokacin da sojoji suka yi yunkurin ceto su.

16 Janairu 2011: Tsohon shugaba Tandja, wanda ake tsare da shi tun bayan juyin mulki a kusa da fadar shugaban kasa, an maida shi wani gidan yari a birnin Yamai.

16 Janairu 2011: Aka fara yakin neman zaben shugaban kasa karo na farko da aka gudanar a ranar 31 ga watan Janairu. Babu wani jami'in sojin da aka yi juyin mulki da shi da zai tsaya takara a zaben.

20 Janairu 2011: Wata kotu ta tuhumi tsohon mataimakin shugaban Majalisar Sojin Kanal Abdoulaye Badie, da wasu sojoji uku da laifin shirya juyin mulki don kifar da gwamnati. 31 Janairun 2011: Shugaban 'yan adawa Mahamadou Issoufou da tsohon Fira minista Seini Oumarou suka tsallake zuwa zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar. 25 Fabrerun 2011: Aka sako wasu 'yan kasashen Faransa da Madagascar da Togo wadanda kungiyar Al-qaeda ta kama tare da 'yan kasar Faransa hudu a watan Satumba.