An sabunta: 10 ga Maris, 2011 - An wallafa a 18:17 GMT

Nijar: Bayan juyin mulkin Fabrerun 2010

Nijer

Hukumomin sojin kasar sun yi alkawarin maida ta kan tafarkin dmokuradiya

Abubuwa masu mahimmanci da suka faru a Nijar tun bayan juyin mulkin watan Fabrerun 2010, a daidai lokacin da ake shirin zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

18 Fabreru 2010: Wani juyin mulki da sojoji suka yi ya hambarar da shugaba Tandja - Wannan ya kawo karshen rikicin da batun tazarcen shugaban ya haifar.

23 Fabreru 2010: Aka bayyana Manjo Salou Djibo a matsayin shugaban Majalisar mulkin sojin kasar.

1 Maris 2010: Aka kafa gwamnatin rikon kwarya ciki harda biyar daga cikin jami'an sojin da suka jagoranci juyin mulki.

31 Oktoba 2010: Aka kada kuri'a kan sabon kundin tsarin mulki da nufin maida kasar kan tafarkin dimokuradiyya.

25 Nuwamba 2010: Gwamnatin soji ta amince da kundin tsarin mulkin da jama'a suka amince da shi a kuri'ar rabagardamar da aka kada.

7 Janairu 2011: Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Al-Qaeda ne suka kama wasu Faransa wa biyu a Yamai, sannan suka kashe su a lokacin da sojoji suka yi yunkurin ceto su.

16 Janairu 2011: Tsohon shugaba Tandja, wanda ake tsare da shi tun bayan juyin mulki a kusa da fadar shugaban kasa, an maida shi wani gidan yari a birnin Yamai.

16 Janairu 2011: Aka fara yakin neman zaben shugaban kasa karo na farko da aka gudanar a ranar 31 ga watan Janairu. Babu wani jami'in sojin da aka yi juyin mulki da shi da zai tsaya takara a zaben.

20 Janairu 2011: Wata kotu ta tuhumi tsohon mataimakin shugaban Majalisar Sojin Kanal Abdoulaye Badie, da wasu sojoji uku da laifin shirya juyin mulki don kifar da gwamnati.

31 Janairun 2011: Shugaban 'yan adawa Mahamadou Issoufou da tsohon Fira minista Seini Oumarou suka tsallake zuwa zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar.

25 Fabrerun 2011: Aka sako wasu 'yan kasashen Faransa da Madagascar da Togo wadanda kungiyar Al-qaeda ta kama tare da 'yan kasar Faransa hudu a watan Satumba.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.