An sabunta: 10 ga Maris, 2011 - An wallafa a 17:20 GMT

Zagaye na biyu na zaben Nijar

Zaben Nijar

Wannan zabe na da matukar mahimmanci ga kasar ta Nijar

Al'umar Nijar za su fita domin kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za a gudanar ranar Asabar wanda zai maida kasar tafarkin dimokuradiyya.

Za dai a fafata ne tsakanin gogaggen dan adawa Mahamadou Issoufou, da kuma tsohon Fira Minista Seini Oumarou, na hannun damar tsohon shugaba Mamadou Tandja wanda sojoji suka yiwa juyin mulki bara.

Ana ganin Mahamadou Issoufou wanda ya dade yana adawa da Tandja shi ne zai lashe zaben bayan da ya samu kashi 31 na kuri'un da aka kada da farko, idan aka kwatanta da kashi 23 da Oumarou ya samu.

Sojoji sun yi alkawarin mayar da kasar tafarkin dimokuradiyya bayan da suka yi juyin mulki a watan Fabrerun bara.

Kawancen siyasa

Jam'iyyar Social Democratic Party ta Issoufou, ta kulla kawance da tsohon Fira Minista Hama Amadou, wanda ya samu kashi 19 a zaben farko.

"Ta la'akari da kawancen mu, muna saran samun kashi 70 cikin dari na kuri'un da za a kada," a cewar Issoufou.

Sai dai abokin hamayyarsa Oumarou, ya yi watsi da wannan tunani, yana mai cewa ba a cin zabe kafin a kada kuri'a.

Dukkan 'yan takarar sun yi alkawarin kawar da talaucin da ya dabaibaye al'ummar kasar ta Nijar da kuma adalci wajen rabon arzikin kasa.

Shugaban gwamnatin sojin kasar Salou Djibo, ya yi kira ga 'yan takarar da su mutunta sakamakon zaben na ranar Asabar.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.