Takaitaccen Tarihin Seini Oumarou

Seini Oumarou Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Seini Oumarou ya yi alkawarin ci gaba da manufofin tsohon shugaba Tandja

An haifi Malam Seini Oumarou a shekarar 1950 a garin Tillaberi daga kabilar Djerma.

Ya rike mukamin minista na kusan shekaru goma a gwamnatin Tandja, kafin daga bisani a nada shi Fira Minista a 2007.

Dan shekaru 60, ya gabatar da kansa a matsayin shugaban bangaren siyasar Tadja.

Shi ne shugaban jam'iyyar National Movement for the Development of Society, kuma ya zo na biyu a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Masu lura da al'amura na ganin Oumarou ya samu goyon bayan jama'ar karkara wadanda tsohon shugaban Tandja ke da farin jini a cikinsu.

Ya fito kiri-kiri ya nemi a saki tsohon shugaban wanda ya ce fursunan siyasa ne.

A lokacin yakin neman zabensa, ya yi alkawarin ci gaba da ayyuka tare da manufofin shuagaba Tandja.

Sai dai ya dandana kudar zamansa a gwamnati. A tsakiyar bara an kama shi na dan wani lokaci kan zargin almubazzaranci da kudaden gwamnati, a wani yunkuri na gyara al'amura da gwamnatin soji ta kaddamar.