Dakarun Gaddafi sun ci gaba da kai hare hare

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mayakan Kanar Gaddafi a kasar Libya

Dakarun dake biyayya ga kanar Gaddafi sun kaddamar da hare hare a wasu muhimman wuraren da dakarun yan tawaye ke rike da ikonsu, wanda ya tilasta masu barin wuraren.

Dakarun gwamnati sun yi ta luguden wuta da tankokin yaki a birnin Ras Lanouf mai arzikin mai dake gabar teku.

Wasu rahotanni daga garin Zawiyya mai nisan mil talatin daga yammacin birnin Tripoli, sun tabbata cewa an yi fatafata da akasarin gidajen dake garin sakamakon kazamin fadan da aka tafka a 'yan kwanakin nan.

Hakazalika sojojin kanar Gaddafi sun ce sun karbe iko a guruwan Bin Jawad da Raslanuf.

A wani taro na matasan dake goyon bayan gwamnati daya halarta, `dan kanar Gaddafi Sa'if Al- Islam Gaddafi ya ce ko a jikinsu, matsin lamban da wasu kasashen duniya ke yiwa kasar, inda ya ce zasu murkushe duk wasu masu adawa.

Ya kuma aike da sako ga sauran 'yan tawayen dake Bengazi inda ya ce su kwan da sanin cewa sojojin gwamnati na zuwa zasu abka musu.