Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Samun kulawa yayin haihuwa

Image caption Akwai bukatar kwararru su kasance tare da macen da ta zo haihuwa

Wani binciken da hukumar kidaya ta Najeriya ta yi da tallafin wasu hukumomi na kasashen waje ya ce samun kulawar da ya kamata daga ma'aikatan lafiya kan rage hadarin kamuwa da cututtuka da matsalalolin da kan taso.

Binciken wanda ya duba shekaru biyar shekarar 2003 zuwa 2005 ya bayyana cewa kashi 39 cikin dari ne na haihuwar da aka samu a wadannan shekarun, kwararrun ma'aikata suka karbi haihuwa a Najeriyar.

Yayinda kashi 35 cikin dari na haihuwar ne ma aka yi su a asibiti.

Haka kuma a cewar binciken kashi sittin da bakwai cikin dari na matan da suka haihu a birane ne, kwararrun ma'aikatan lafiya suka karbi haihuwar, kuma kashi sittin ciki dari ne matan ne suka haihu a asibiti.

A yankunan karkarar kasar kuwa, binciken yace kashi 27 cikin dari ne na matan da suka haihu a shekaru biyar din da akayi binciken, kwarraun ma'aikatan lafiya suka karbi haihuwar, yayinda kashi 24 cikin dari na matan karkarar da suka haihun ne suka haihu a asibiti.

Akwai dai bukatar kulawa ta musamman da mace a lokacin da ta zo haihuwa, domin kaucewa irin wadancan matsaloli.