An bude wuta kan masu zanga zanga a Saudiyya

Image caption Jami'an 'yan sanda a kasar Saudiyya

'Yan sanda a kasar Saudiyya sun bude wuta kan masu zanga zanga a birnin Qatif dake gabashin kasar.

Rahotanni na nuna cewa 'yan sanda sun yi amfani da gurnetin duwatsu suka harba shi sama, da nufin tarwatsa masu zanga zangar dake kiran da a gudanar da sauye sauye a masarautar kasar ta Saudiyya.

Babu dai wanda ya rasa ransa a lamarin sai rahotanni sun ce a kalla mutum guda ne ya jikkata.

Wasu mutane ne suka bijirewa gargadin da gwamnatin kasar ta yi, na hana duk wata zanga zanga inda suka gudanar.

Ana dai ta amfani da shafin internet domin shirya wata babbar zanga zanga a yau Juma'a.