Zanga-zanga mafi girma a Yemen

Shugaba Abdallah Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Abdallah ya yi alkawarin kawo sauye-sauye amma 'yan adawa sun ki

Dubun dubatar jama'a ne suka fita kan tituna domin zanga-zangar adawa da gwamnati a Sana'a babban birnin kasar Yemen bayan idar da sallar Juma'a.

Masu zanga-zangar wadanda suka cika titunan birnin na Sana'a, na bukatar shugaba Abdallah Saleh ya yi murabus.

Suma dai masu goyon bayan gwamnatin ta Mr Abdallah sun yi tasu zanga-zangar.

Wakilin BBC a kasar ya ce za a iya cewa wannan ita ce babbar zanga-zanga da aka yi a kan titunan kasar domin nuna adawa da shugaba Abdallah Saleh.

Shugaba Abdallah Saleh dai ya shafe shekaru talatin da biyu yana mulkin kasar ta Yemen.