Yiwuwar zaben shugaban Najeriya zagaye na biyu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zaben Najeriya na shekarar 2011

A Najeriya, yayin da yanzu haka ya rage kwanaki kadan kafin a gudanar da zaben kasar, wani al'amari da masu fashin baki suka fara nazari akai shine batun yiwuwar zuwa zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

Masana na hasashen cewa mai yiwuwa a samu hakan ne muddin daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa daga kowacce jam'iyya ya gaza samun kashi ashirin da biyar cikin dari na kuri'un da za'a jefa a jihohi ashirin da hudu cikin jihiohin kasar ashirin da shida da kuma birnin tarayya Abuja.

Malam Abubakar Kari Masani kan kimiyyar siyasa, ya ce "akwai yiwuwar kaiwa ga zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Najeriyar a bana".

Sai dai hukumar zaben kasar wato INEC ta ce ta yi kyakkyawan tanadi na gudanar da zaben zagaye na biyu matukar aka samu yanayin da zai kai ga har sai an gudanar da zaben shugaban kasar zagaye na biyu.