An kama mutane dauke da bama-bamai a Jos

Jami'an tsaro a Najeriya
Image caption Jami'an tsaro sun cafke bama-bamai a Jos

A Nijeriya, hukumomin tsaro a jihar Filato sun kama wata babbar motar dakon kaya ta yi lodin bama-bamai zuwa Jos babban birnin jihar.

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa mai aiki a jihar ce ta kama wannan mota, da kuma mutane biyu wadanda ke tafe da ita cikinsu harda wani dan sanda, yayin da suke gab da shiga Jos daga hanyar Kaduna.

A cewar rundunar tsaron, mutanen sun shaida mata cewa za su kai wadannan abubuwa masu fashewa ne ga wani kamfani mai suna Dewang da ke birnin na Jos.

Hukumomin tsaron sun ce suna ci gaba da bincike da zummar gano makasudin aiko da bama-baman cikin jihar mai fama da tashe-tashen hankula.