Fashewa a tashar nukiliyar Japan

Japan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan tashar na da mahimmanci ga kasar Japan

A Japan, an ji babbar karar fashewar abubuwa a wata tashar nukiliya, wadda mummunar girgizar kasar da aka yi a ranar Juma'a ta lalata.

Hukumomin Japan din sun fadada yankin da za a kwashe jama'a daga ciki, a kewayen tashar nukiliyar da ta lalace.

Yanzu haka kuma ana gudanar da gagarumin aikin kai dauki a Japan din, bayan mummunar ambaliyar teku da girgizar kasar da aka yi.

An ce kawo yanzu mutane fiye da dubu guda ne aka tabbatar sun hallaka, kuma fiye da dubu dari biyu suna zaune a wasu wuraren wucin-gadin da aka kebe.

A lokacin da girgizar kasar ta afku, tashar nukiliyar ta Fukushima ta daina aiki nan take kamar yadda aka tsara ta.

Sai dai injinan dake baiwa tashar wuta domin rin wannan hali na ko-ta-kwana sun daina aiki.

Babban Sakateren gwamnatin Japan Yukio Edano, ya shaida wa manema labarai cewa babu tabbas ko matakin da masana su ka dauka na rage matsalar da tashar ke fuskanta ne ya haifar da fashewar.

Fira ministan Japan Naoto Kan, ya ziyarci inda wannan bala'i ya fi muni, inda ya ce"na ga gidajen da igiyar tsunami ta yi awan gaba da su da kuma wuta a yankunan da duwatsu suke".