Fiye da mutane 1000 suka mutu a Japan

Barnar da girgizar kasa da ambaliyar ruwa suka yi a Japan
Image caption Hukumomi sun ce fiye da mutane 1000 ne masifar ta shafa

Gwamnatin kasar Japan ta ce fiye da mutane 1000 ne suka mutu sakamakon girgizar kasa tare da ambaliyar ruwan teku da ta abkawa kasar ranar Juma'a.

Akasarin wadanda suka mutu dai ambaliyar ruwan ce ta tafi da su a yankunan da ke gabar tekun da ke arewaci da gabashin birnin Tokyo.

Yanzu haka ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da daukacin gidajen da ke garin Ri-ku-zen-ta-kada inda fiye da mutane dubu ashirin ke zaune.

Wata 'yar Najeriya, Bilkisu Sa'idu da ke birnin Tokyo ta shaidawa BBC cewa girgizar kasar ta riske su ne a lokacin suna makaranta.