Yunkurin takunkumin hana shawagi a Libya

Shugaban kungiyar kasashen Larabawa, Amr Moussa, ya goyi bayan a hana jiragen sama yin shawagi a sararin samaniyar Libiya.

Ya kuma ce, yana son kasashen Larabawar su taka rawa wajen tabbatar da takunkumin.

Amr Moussa ya bayyana hakan ne, a taron kungiyar a birnin Alkahira, akan rikicin kasar ta Libiya.

Babbar jami'ar diplomasiyyar Tarayyar Turai, Catherine Ashton, za ta birnin Alkahirar, domin tattaunawa a kan irin martani na bai-dayan da za a mayar.

A can Libiyar kuma, rahotanni sun ce, a halin yanzu dakarun Kanar Gaddafi ne ke iko da garin Ras Lanuf mai tashar mai, wanda hakan ya tilasta wa 'yan tawaye kara janyewa zuwa gabashin kasar.