Zabe na ci gaba da gudana a Nijar

Wani da ya kada kuri'arsa a Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yau ake zabe zagaye na biyu kuma na karshe a Nijar

A jamhuriyar Nijar kimanin mutane miliyan 6 da rabi ne ke kada kuri'a a yau, domin zaben shugaban kasar na gaba.

Ana takara ne tsakanin Alhaji Seyni Oumarou na MNSD- NASSARA, da kuma Alhaji Mahammadou Issoufou na PNDS Tarayya.

Zaben shi ne zai mayar da kasar bisa tafarkin dimokradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a bara, sakamakon kiki-kakan siyasar da aka samu.

To ya zuwa yanzu dai zaben na gudana lafiya, kodayake daga nude rumfunan zaben zuwa tsakar rana, ba a samu fitar jama'a sosai ba.

Dukkan 'yan takarar shugaban kasar biyu sun yi alkawarin rungumar sakamakon zaben .