Majalisar dinkin duniya za ta tattuna kan Kenya

Zauren majalisar dinkin duniya Hakkin mallakar hoto REUTERS

Majalisar Dinkin Duniya za ta gana a makon gobe don tattaunawa kan kalubalantar da kasar Kenya ta yi game da binciken rikicin siyasar da ya barke bayan zaben kasar a shekarar 2008.

Kotun hukunta masu aikata manyan laifuffuka ta duniya ta mika sammaci ga wasu 'yan kasar Kenya su shida ne, wadanda ake zargi da hannu a rikicin, yayin da kuma kasar Kenya ke neman a dakatar da sauraren karar, a kuma barta ta tuhumi mutanen a kasar ta.

Wadanda zasu halarci taron Kwamiitin tsaro dai sun hada da wakilai daga kasar ta Kenya da kuma kungiyar tarayya Afrika AU.

Sai dai jami'an diplomasiyya sun ce kasashe kalilan ne ke goyon bayan bukatar da kasar Kenya ke nema.