An fara zabe a jamhuriyar Nijar

Tutar jamhuriyar Nijar
Image caption An fara zabe a Nijar

Jama'a sun fara fitowa domin kada kuri'unsu a zagaye na biyu na zaben da za a gudanar a jamhuriyar Nijar.

Kimanin mutane miliyan shida da rabi ne zasu kada kuri'ar zaben shugaban kasa.

'Yan kasar ta Nijar za su zabi shugaban kasar ne tsakanin 'yan takara biyu da zasu fafata, wato Alhaji Mahamadou Isufu na jam'iyyar Pe-N-De-S-Tarayya da Alhaji Seini Umaru na jam'iyyar M-NeS-De-Nasara.

Tuni dai hukumar zabe mai zaman kanta CENI ta ce ta kai kayayyakin zabe a kowane sashi na kasar, yayinda shugaban kasa ya yi kira ga 'yan takarar biyu dasu bi a hankali don ganin zaben ya gudana cikin lumana.