Amurka ta goyi bayan kasashen larabawa

Shugaban Amurka Barack Obama Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Gwamnatin Amurka ta ce tana goyon bayan kiran da kungiyar kasashen larabawa suka yi na neman hana shawagin jiragen sama akan kasar Libya.

Fadar gwamnatin Amurkan ta ce yarjejeniyar da kungiyar ta cimma na neman kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, ya tabbatar da sanya wannan haramci ga kasar Libya, ya karfafa matsain lamba na kasashen duniya kan Kanar Gaddafi.

Youssef Ben Alawi, shi ne ministan harkokin waje na Yemen, ya ce kungiyar kasashen larabawa ta bukaci kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya sanya matakin hana shawagin jiragen sama akan Libya ne, saboda ta kare al'ummomin kasar da kuma sauran 'yan wasu kasashen da ke zaune a Libya.

Har yanzu dai ana ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun da ke goyon bayan Kanal Gaddafi da 'yan tawaye.