Akwai yiwuwar narkewar nukiliya a Japan

Ma'aikatan da ke kwashe mutane daga yankin da tashar nukilya ta ke Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Akwai yiwuwar narkewar tashar makamashin nukiliya

Gwamnatin Japan ta ce akwai yiwuwar narkewar nukiliya a wata tasharsa ta yankin Fukushima sakamakon mummunar girgizar kasar da ta fadawa yankin.

Sakataren gwamnatin kasar Yukio Edano, ya ce injinan da ke hana wasu na'urorin da ke tashar nukiliyar daukar zafi sun daina aiki, lamarin da ya yi sanadiyar fitar da hayaki da ke tiriri a tashar nukiliyar.

Gwamnatin Japan ta umurci jama'ar da ke kusa da tashar nukiliyar da su fice daga yankin, kana ta ci gaba da basu tabbacin cewa ba za su kamu da wata cuta ba sakamakon shakar hayakin da ke fitowa daga tashar nukiliyar.

Kimanin mutane dubu dari biyu ne ke zaune a yankin.