Damuwar duniya game da hadarin nukiliyar Japan

Angela Merkel Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Angela Merkel

Hadarin nukiliyar da kasar Japan ta fada ciki, sakamakon girgizar kasar ranar Juma'a ya sake tayar da damuwa a sauran kasashen duniya.

A Jamus, Shugabar Gwamnatin kasar, Angela Merkel, ta bayyana matsalar ta Japan a matsayin wani abun da ya kamata ya farkar da duniya.

Ta ce a halin yanzu za a sake nazartar matsayin matakan kariyar da ake da su a tashoshin nukiliyar kasar Jamus.

A Amurka , wani tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata Joe Lieberman, ya ce gwamnatin Amurka na bukatar dakatar da gina tashoshin nukiliya har sai an koyi dukanin darasi daga abinda ke faruwa a Japan.