'Yan tawaye sun janye daga garin Brega na Gabashin Libya

Wasu dakarun 'yan tawaye a Ras Lanuf Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu dakarun 'yan tawaye a Ras Lanuf

An tilastawa yan tawaye a Libya janyewa daga garin Brega dake a gabashin kasar bayan da dakarun dake biyayya ga Kanar Gaddafi suka yi masu ruwan bama bamai.

Garin Brega shi ne gari na biyu da 'yan tawaye ke rike da shi da ya fadi bayan muhimmin garin nan na Ras Lanuf mai tashar ruwan fitar da mai.

A babban sansanin 'yan tawayen na karshe a yammacin Libya, Misrata, an bayar da rahoton jin amon wutar tankokin yaki a wajen birnin.

Wani Kakakin sojin Libya, Milad Hussein ya ce a halin yanzu babu yantawaye a galibin yankunan da aka yi gumurzu.

A halin yanzu kuma Faransa ta ce, tana son hanzarta kokarin diplomasiya domin saka shiyar hanin zurga- zurgar jiragen sama a sasararin samaniyar Libya.