HRW ta yi tsokaci kan zaben Nijeriya

Wasu masu zabe a Nijeriya
Image caption Wasu masu zabe a Nijeriya

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta nemi majalisar dokokin Naijeriya da ta gaggauta kafa wata hukumar ladabtar da masu aikata laifuffukan siyasa a kasar.

A wata sanarwar hadin guiwa da ta fitar a yau tare da kungiyar lauyoyi ta Nigeria, NBA, kungiyar ta Human Rights Watch ta ce ta haka ne kawai za a samu zarafin rage munanan laifufukan da ake tafkawa da suka danganci kashe-kashe da magudin zabe a kasar.

Sanarwar ta kara da cewa Nijeriya na bukatar tabbatar da martabar zabubukan da zaa yi a cikin watan Afrilu mai zuwa ta hanyar kaucewa tashin hankali da razana abokan hammaya da kuma magudin zabe.

Sanarwar ta ce mutane fiye da hamsin aka kashe a tashin hankalin dake nasaba da siyasa tun cikin watan Nuwamban da ya gabata.