Ana cigaba da bayyana sakamakon zaben Nijar

Wata rumfar zabe a Nijar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata rumfar zabe a Nijar

A Jumhuriyar Nijer, hukumar zabe mai zaman kanta, CENI tana cigaba da tattarawa, tare da bayyana sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da aka gudanar a jiya.

Har zuwa Magariba dai hukumar zaben ta bayyana sakamakon gundumomi dari da 8 ne daga cikin dari 2 da 66.

Hukumar ta ce aikin tattara sakamakon na tafiya lafiya, kuma tana as ran bayyana sakamakon karshe nan da zuwa gobe Litinin.

An dai fafata ne tsakanin dan takarar jam'iyyar PNDS-Tarayya, Alhaji Mahamadou Issoufou da na jam'iyyar MNSD-Nasara, Alhaji Seini Oumarou.