Kasar Japan na fadi tashi da matsalar Nukiliya

Tashar nukiliya ta Fukushima Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An saken jin fashewar wani abu a Japan

Mahukuntan kasar Japan na ta kokarin sanyaya tukwanen makamashin nukiliya dake wata tashar makamashin da ta lalace bayan girgizar kasa da ambaliyar ruwan teku ta tsunamin a kasar ranar juma'a.

Ma'aikata a tashar makamashin nukiliyar ta Fukushima wadda ta lalace sun yi gargadin cewa tukwanen na iya narkewa bayan da karafan tukunyar makamashin ta 2 suka fito waje.

Tuni gwamnati ta bada sanarwar samarda ruwa a tashar tare da daukar matakan kare jama'a.

Sakataren majalisar zartarwar Japan Yukio Edano, ya ce, " mun bada umarnin kwashe mutanen dake a yankunan dake da nisan kilo mita 20 da tashar."

Wakilin BBC kan muhalli ya ce babban abu ne hakan ke iya haifarwa. Kuma ya ce abin tambayar shi ne ko za'a iya hana narkewar karafen tukunan.

Gwamnatin kasar Japan ta ce ba wani hadari mai yawa da turirin da ya tashi a tashar makamashin nukiliya ta Fukushima zai haifar, kamar yadda wani babban jami'in gwamnatin Japan din ya bayyana.

Jirgin ruwan Amurka da ke dakon jiragen sama dake da nisan kilo mita dari da hamsin a gabar ruwan kasar ya dan gurbata da tururin makamshin nukiliyar.

Kuma tuni aka kara matsar da jirgin ruwan da ya je domin ayyukan taimako a kasar.

Kasashe da dama na ci gaba da nuna damuwarsu game da kariya a tashoshin nukiliyarsu, sabilida halin kakanikayin da aka shiga ga me da nukiliyar Japan.

Kasar Switzerland ta dakatar da shirye shiryenta na gina sababbin tashoshin nukiliya har sai ta gudanar da cikakken shiri game da kariya.

Shi ma Pirayim ministan India, Manmohan Singh ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa zaa duba dukkan irin matakan kariyar da ake da su a tashoshin makamashin nukiliyar kasar domin tabbatar da cewa za su iya haye matsalar girgizar kasa da ambaliyar ruwan teku ta tsunami: