Tukunya a cibiyar makamshin Japan ta yi bindiga

Hakkin mallakar hoto AP

Gwamnatin Japan ta yi gargadin cewa wadanda ke nisan kilomita talatin daga cibiyar makamashin nukiliya da su ci gaba da kasancewa a cikin gida, musamman bayan da wuta ta tashi a karo na uku.

Prime Ministan kasar yace na'urorin da ke bayyana halin da ake ciki na nuni da irin karfin girgizar da cibiyar nukiliyar ke fitarwa.

Akwai hadarin cewa makamashi da wasu sinadarai dake malala daga bututan tukunyar makamshin nukiliya ta biyu na da matukar illa ga rayuwar bil adama.

Ya bayyyana cewa an kwashe duka ma'aikatan wurin saura 'yan kadan da ke ci gaba da yunkurin sanyaya tukwanan da kuma kokarin rage girman hadarin da ka iya biyo baya.

Ya kara da cewa ya kamata duka wadanda ke nisan kilomita ashirin da ga inda cibiyar makamashin nukiliyar ta ke da su kauracewa wajen.

Sa'o'i biyu bayan wutar da ta tashi a safiyar yau a tukunya ta biyu, karfin girgizar da ke faruwa ana jin ya ninka yadda ya kamata sau takwas, wato kwatankwacin irin abinda ya kamata al'umma su fuskanta a cikin shekara guda.

Sai dai kuma hukumar makamashi ta kasar ta bayyana zargin cewa tashin wutar ya lalata bututun cikin tukunyar makamashin ta biyu, wanda kuma hakan ka iya sanyawa ya kasance hadari mafi girma akan sauran biyun da suka faru a baya da ake tunanin sun barnata cibiyar.