An hallaka wani malami a Maiduguri

Jami'an tsaron Najeriya
Image caption Ana fuskantar kalubalen tsaro a Najeriya

An harbe har lahira wani malamin addinin musulunci a birnin Maiduguri na jihar Bornon Najeriya.

Wasu shaidu sun ce wasu mutane ne suka farma malamin, Ibrahim Ahmed Abdullahi Bolori, a kusa da wani masallaci a Maiduguri.

Shi dai malamin ya yi fice wajen sukar kungiyar nan ta Boko Haram da ke kai hare-hare a Maiduguri tun daga shekarar 2009, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama wadanda akasarin su jami'an 'yan sanda ne.

Matsalar rashin tsaro ta yi kamari a kasar ta Najeriya, musamman a yanzu da babban zaben kasar ke gabatowa.