Mahamadou Issoufou ya lashe zaben Nijar

Mahamadou Issoufou
Image caption Mahamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS shi ne jarogaran 'yan adawa

Hukumar zabe a Jamhuriyar Nijar ta bayyana jagoran 'yan adawa Mahamadou Issoufou, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da kashi 57 cikin dari.

Mr Issoufou ya sha kayi a zabuka biyun da su ka wuce a hannun tsohon shugaba Tandja, wanda sojoji suka kifar a bara.

Dan takarar jam'iyyar Tandja Seini Oumarou ya samu kashi 42 cikin dari na kuri'un da aka kada.

An shirya zaben ne domin maida kasar tafarkin Dimokuradiyya.

Tuni dai abokin takarar Mahamadou Issoufou wato Sieni Oumarou ya amince da kayen da ya sha.

" Bani da niyar daukaka kara a zaben, kuma ina wa Mahamadou Issoufou murna." In ji Seyni Oumarou

Takaitaccen tarihin Mahamadou Issoufou

An haifi Mahamadou Issoufou a shekarar 1952 a garin Tahoua inda Hausawa ke da rinjaye. Dan shekaru 59, Shi ne shugaban jam'iyyar Niger Party for Democracy and Socialism.

Ya taba zama Fira Ministan kasar daga 1993 zuwa 1994, sannan ya zama kakakin Majalisar Dokokin kasar daga 1995 zuwa 1996.

Mahamadou Issoufou, wanda injiniya ne da ke aiki da kamfanin hakar ma'adinai na Faransa Areva, wanda ke aikin hako ma'adanai a Arewacin kasar.

Ya tsaya a dukkan zabukan shugaban kasa hudu da aka gudanar a kasar ba tare da yin nasara ba, inda Tandja ya ka da shi a 1999 da 2004.

Ya kasance jagoran 'yan adawa a lokacin mulkin shugaba Tandja.

A baya an zarge shi da laifin halatta kudaden haram - an kama shi bayan komawarsa gida, amma daga bisani aka sake shi.

Issoufou, wanda ake wa lakabi da Zaki -- ya ce yana fatan nunu wa duniya cewa Nijar wacce ke da arzikin ma'adanai, ba matalauciyar kasa ba ce, sai dai kawai ba a tafiyar da al'amura kamar yadda suka kamata.

Ya yi alkawarin gyara tsarin aikin gwamnati da samar da tsaro a kasar da 'ya'yan kungiyar Al-qaeda a Yankin Maghreb ke garkuwa da 'yan kasashen waje.

Ya samu kashi 36 da digo 6 cikin dari na kuri'un da aka kada a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar.