Najeriya:Amfani da waya don magance magudi

A Nigeria wasu masu sa ido akan zabe sun kaddamar da wani tsarin yin amfami da wayar salulu don tsegunta hatasyiniya ko magudin zabe a zabukanan kasar da ke tafe.

Cibiyar wanzar da dimokaradiyya a Nigeria wato National Democratic Institute da kungiyar kwadago, tare da hadin gwiwayar wasu kungiyoyi masu zaman kansu ne su ka kaddamar da wannan tsari.

Kungiyoyin sun ce za su yi amfani da masu sa ido dubu hudu da dari biyar a zabe mai zuwa, kuma su na kira ga jama'a da su yi amfani da wayoyinsu na salula don tsegunta musu duk wani nau'in magudi ko wani tashin hankali a lokacin zabe.

Wannan dai shine karo na farko da za'a ayi amfani da wannan tsari a Nigeria.