Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kauracewa kada kuri'a a zabukan Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sai dai jama'a da dama sun fito domin yin rijistar zabe a kasar

A Najeriya, wata matsalar da ke damun harkar zabe a kasar ita ce yadda wasu `yan kasar ke kin fita kada kuri`unsu a lokutan zabe.

Bincike dai ya nuna yawan `yan kasar da kan fita kada kuri`a ba ya zarta rabin wadanda akan yi wa rajistar kada kuri`ar.

Kuma wannan ya sanya Najeriya a cikin jerin kasashen duniya da suka fi sauran kasashe yawan masu gudun kada kuri`a.

Sai dai a wannan shekarar da kasar ke fuskantar babban zabenta, `yan kasar sun nuna wata dabi`ar da ba kasafai sukan yi ba, inda miliyoyin `yan kasar suka fita kwansu da kwarkwata don yin rajistar zabe.

Lamarin da ya sanya wasu ke ganin watakila dabi`ar `yan kasar ta kin fita kada kuri`a za ta sauya a wannan karon.

Wakilin BBC Ibrahim Isa ya hada mana wannan rahoton na musamman: