'Yan tawaye sun kame garin Brega a Libya

Dakarun 'yan tawayen da suka kwace garin  Brega Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Dakarun 'yan tawaye a birnin Brega na Libya sun ce sun fatattaki sojojin da ke goyon bayan kanar Gaddafi inda suka sake shiga garin.

Tun da farko a jiya ne dai sojojin da ke goyon bayan Gaddafi suka yi ta luguden wuta akan 'yan tawayen, wanda ya tilasta musu ja da baya.

Sai dai yanzu sun ce wasu dakarun su da suka zo daga Benghazi, garin da 'yan tawayen ke da karfi sun sake karbe iko da Brega.

Wakilin BBC ya ce ana ganin ba mai yiwuwa ba ne dakarun da ke adawa da gwamnati su sake samun galaba har sai sun samu taimako kai tsaye daga kasashen waje, wanda kuma, da kamar wuya.