Tururin da ke tashi a Fukushima ya lafa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Zafin tururi ya sa ala tilas an tsagaita yunkurin da ake yi na sanyaya tukwanan makamashin nukiliyar Japan, wadanda bala'in girgizar kasa da mahaukacin guguwa mai hade da ruwa ta Tsunami suka yiwa barna.

Sai dai yanzu haka wani mai magana da yawun Gwamnatin Kasar ya bayyana cewa adadin tururin na raguwa.

Inda ya kara da cewa farin hayakin da ake gani na tashi daga cibiyar a sanadiyyar ruwan da ake amfani dashi ne wajen sanyaya tukwanan.

Tun ranar Juma'ar da ta gabata ma'aikata ke ta faman kokarin sanyaya tukwanan makamashin nukiliya hudu da ke cibiyar makamashin Fukushima.

Sai dai kuma tururi da bindiga da tashin wuta sun yi ta kawo musu cikas.

Hukumar makamashi ta kasar ta bayyana cewa ma'aikatan cibiyar sun ce wuta ta dauke a can.

A jiya talata kuwa tururi daga tukwanan makamashin ya yi ta tashi.

Sai dai daga baya ya ragu amma duk da haka zai iya yin barazana ga rayuwar bil adama.

Ma'aikatan cibiyar makamashin dai na ci gaba da kwarara ruwan teku a tukwanan domin sanyaya su, su koma yanda suke.

Kuma ana ganin cewa idan har aka dade ana yin haka, to akwai yiwuwar samun nasarar sanyaya bututan da ke cikin tukwanen.

Sai dai duk da haka bulbular turarin na damun al'ummar kasar ta Japan da ma makwabtan kasashe da ke Allah- Allah wajen ganin komai ya koma yanda yake.