Wasu kungiyoyi na wayar da kai akan zabe a Najeriya

Najeriya kasa ce da ke kunshe da kungiyoyi masu zaman kan su da dama.

A cikin ayyukan da wasu daga cikin kungiyoyin kan ce suna yi shi ne na kokarin wayar da kan jama'a a bisa harkokin da su ka shafi siyasar Kasar da gudanar da zabe na gari domin samun sahihan Shugabanni.

To amma duk da ikirarin wadannan kungiyoyi wasu a Najeriya sun sha nuna cewa kungiyoyin na gudanar da ayyukansu ne a birane, in da su kan bar mutanen karkara cikin duhu.

Sai dai su kungiyoyi sun bayyana cewa ba haka al'amarin ya ke ba.