Gwamnan jahar Katsina ya tsallake rijiya da baya

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, ya tsallake rijiya da baya, bayan wani hadarin mota da ya hallaka mutane akalla biyar.

Gwamnan na Jihar Katsina yana kan hanyarsa ne ta zuwa taryen Shugaba Goodluck Jonathan, a lokacin da motar da ya ke ciki ta yi taho mu gama da wata motar pasinja, akan hanyar Katsina zuwa Daura.

An ce daga bisani gwamnan ya samu damar halartar taron siyasar da shugaba Goodluck Jonathan yayi a Katsina.