Dokar hana zirga zirgar jirage a Libya

Hakkin mallakar hoto AP

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na kira game da saka dokar haramcin hana zirga zirgar jirage a Libya, tare kuma da tsauraran takunkumi akan jami'an kasar.

Kwamitin ya bayyana cewa wannan wani martani ne ga wata bukata ta kungiyar kasashen Larabawa domin daukar wannan mataki.

Sai dai kawo yanzu akwai rarrabuwar kai a kwamitin game da amfani da soji a kasar ta Libya.

Jakadun Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa kudurin zai haramtawa duk wasu jirage bi ta sararin samaniyar Libya, tare kuma da yin kira ga mambobin kasashe su tabbatar da cewa Libya ta yi biyayya ga haka.

Kamar dai yanda mambobin kwamitin suka bayyana, sun ce za su so ganin cewa kasashen Larabawa sun taka rawa a wannan matakin da ake son dauka.

Sai dai kawo yanzu baya ga kasashen Russia da Sin, wadanda dama can su ka ki amincewa da amfani da soji a kasar, akwai sauran wasu kasashen dake adawa da wannan kudurin.

Jamus ta bayyana cewa har yanzu akwai ayoyin tambayar da ba'a amsa ba, sannan kuma Amurka har yanzu ba ta bayyana matsayar ta ba.