Hillary Clinton ta soki lamirin Bahrain

Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Clinton ta ce Bahrain ba ta kyauta ba

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta soki mahukuntan Bahrain bisa tura sojoji su murkushe masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Mrs Clinton ta ce ta kadu da abin da ya faru, kuma kamar yadda ta ce gwamnatin Bahrain ba ta kyauta ba.

Hillary Clinton ta ce ba su goyan bayan yin amfani da karfi a kan masu zanga-zanga, ba su kuma goyon bayan su ma masu zanga-zanga su yi amfani da karfi.

Ta ce abu mafi a'ala shi ne bangarorin biyu su sasanta cikin ruwan sanyi.