China na yunkurin taimakawa Japan

Hakkin mallakar hoto AFP

Kwanaki shida bayan girgizar kasa da kuma tsunamin da suka auku a Japan, China ta bukaci makwabciyar ta da ta bata cikakkun bayanai game da matsalar makamashi Nukiliya da kasar ke fuskanta.

Jiragen sojin kasar Japan masu saukar angulu sun yi ta zuba ruwa kan tukwanen Nukiliya biyu da suka lalace a tashar makashin da ke Fukushima.

Aiki irin wannan a baya dai ya haddasa karuwar tururin Nukiliya a saman tashar.

Mahukunta a kasar dai na ta kokarin sanyaya tukwanen Nukiliya guda hudu a tashar.

Mahukuntan sun ce yanzu kam an tabbatar da cewa kusan mutane dubu biyar da dari biyu ne suka halaka sakamakon girgizar kasa da Tsunami, yayinda kimanin mutane dubu goma suka bace.

Tsananin sanyi kuma, ya sake jefa wadanda suka tsira cikin mummunan yanayi.

Kodayake rahotanni na nuna cewa kayayyakin agaji na kaiwa gare su, sai dai Gwamnan yankin na Fukushima, inda tashar nuclear da ta yi matukar lalacewa take, ya bayyana damuwarsa ta cewa sansanin da ake kai mutanen da suka tsira, ba bu muhimman kayayyakin da ake bukata, inda ya ce hatta abinci ma baya isa.

Amurka kuma ta bayyana damuwar ta game da matsalar dake faruwa a tashar Nukiliya ta Fukushima da ke kasar Japan, inda abubuwa suka yi ta fashewa tare da tashin gobara, tun bayan barnar da girgizar kasa ta Tsunami su ka yi wa tashar a makon jiya.

Shugaban hukumar kula da makamashin nuclear Amurka Gregory Jaczko ya bayyana cewa yana tsammanin daya daga cikin tukwanen Nukiliyar ta fashe.

An baiwa wasu jamian sojin Amurka da ke Japan magunguna don kare su da ga illar tururin nukiliyar, kuma Amurkar ta yi kira ga 'yan kasar ta da ke zaune a yankunan da basu zarce tazarar kilomita 80 daga tashar makamashi ta Fukushima ba, da su fice daga yankin.