Amurka na nuna damuwa kan hadarin Fukushima

Sakataren Makamashin Amurka, Steven Chu
Image caption Sakataren Makamashin Amurka, Steven Chu

Amurka ta bayyana damuwa a game da matsalar tashar makamashin nukiliya ta Fukushima a kasar Japan, wadda ta yi matukar lalacewa, sakamakon mummunar girgizar kasar da aka yi a makon jiya.

Gwamnatin Amurka ta yi kira ga 'yan kasarta dake zaune a nisan kilomita tamanin da tashar da su bar wajen.

Sakataren makamashi na Amurkan ya ce da alama munin lamarin ya fi na wanda ya faru a tsibirin Three Mile dake jihar Pennsylvania a shekarar 1979.

Shugaban hukumar makamashi ta Majalisar Dinkin Duniya, Yukio Amano ya ce yanzu haka an tabbatar da lalacewar tukwane uku a tashar makamshin ta Fukushima.