Fargaba game da bazuwar birbishin nukiliya a Japan

Ma'aikatan nukiliya a Japan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ma'aikatan nukiliya a Japan

Mahukuntan kasar Japan sun ce tilas ta sa suka yi watsi da aikin watsa ruwa ta jirage masu saukar angulu, domin sanyaya tukunyar nukiliyar da ta dau zafi, a tashar da ta lalace, sakamakon ambaliyar ruwan Tsunami da kuma girgizar kasa.

Rahotanni daga kasar ta Japan sun ce an dakatar da aikin ne, saboda fargabar da ake ta tashin burbushin makamashin nukiliya zuwa sama.

Tun da farko kamfanin makamashi na Fukushima ya kwashe dukan ma'aikatansa sabili da karuwar da birbishin nukiliyar, to amma yanzu sun koma aiki.

Sarkin sarakunan kasar, Akihito ya ce ya damu kwarai da matsalar da ake fama da ita a tashar nukiliyar ta Fukushima Daiichi.

Har yanzu ba a ji duriyar dubban jama'a da bala'in Tsunami da girgizar kasa ya ritsa da su ba.

Wasu dubban daruruwa kuma suna zaune ne a gidaje ba tare da wutar lantarki ba.

A na kuma fama da dussar kankara da sanyi a wasu garuruwan da abin ya shafa.